Vidal ya yi hadari da motarsa a Santiago

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Vidal ya yi da ya sannin aika-aikar

'Yan sanda sun sako dan kwallon Juventus da Chile, Arturo Vidal da aka kama bayan ya sha giya ya yi hadari da motarsa.

Dan shekaru 28, wanda shi ne ya fi kowanne dan kwallo zura kwallaye a gasar cin kofin Copa America da ake bugawa a kasarsa, ya yi hadarinne da motarsa kirar Ferrari a ranar Talata da daddare a birnin Santiago.

Vidal wanda ya kurje, an kwace masa lasisin tukinsa amma zai ci gaba da buga wa Chile kwallo.

"Na yi abin kunya," in ji Vidal wanda idonunsa ke cike da kwalla.

Kocin Chile, Jorge Sampaoli ya ce maganganun mutane ya yi yawa a kan batun.