Messi ya jajantawa Neymar bisa jan kati

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Brazil ta ce za ta daukaka kara kan dakatar da Neymar daga buga wasanni da aka yi

Kyaftin din Argentina Lionel Messi ya jajantawa Neymar bisa dakatar da shi da aka yi daga buga wasannin gasar Copa America da Chile ke karbar bakunci.

An bai wa Neymar jan kati bayan da ya yi karo da dan wasan Colombia a karawar da Brazil ta samu nasara da ci1-0, hakan ya sa aka dakatar da shi daga buga wasanni hudu.

Sai dai kuma hukumar kwallon kafar Brazil tana tunanin daukaka kara kan hukuncin da aka yanke wa Neymar.

Messi ya ce "Neymar abokina ne kuma ban ji dadin dakatar da shi da aka yi daga wasannin ba, domin fitatcen dan kwallo ne mai mahimmaci a cikin tawagar 'yan wasan Brazil".

Colombia za ta fafata da Peru a wasannin rukuni na uku, yayin da Brazil wacce ke da maki uku za ta kara da Venezuela da ita ma ke da maki ukun ranar Lahadi.