Liverpool ta dauki Joe Gomez daga Chalton

Image caption Joe shi ne dan kwallo na hudu da Liverpool ta dauko zuwa Anfield

Kungiyar Liverpool ta dauki dan kwallon Charlton mai tsaron baya Joe Gomez kan kudi £3.5m.

Dan kwallon mai buga wa tawagar Ingila ta matasa 'yan kasa da shekaru 19 wasanni, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru biyar a Anfield.

Dan kwallon, mai shekaru 18, zai yi wasannin share fagen tunkarar Premier da Liverpool, kafin ta bayar da shi aro ga Derby wacce ke sha'awar dan wasan tun a baya.

Gomez ya lashe kofin matasa 'yan kasa da shekaru 17 ta nahiyar Turai da Ingila ta dauka a Malta a shekarar 2014.

Dan wasan shi ne dan kwallo na hudu da Liverpool ta kawo Anfield bayan James Milner da Danny Ings da kuma mai tsaron raga Adam Bogdan.