Inter Milan za ta dauki Kondogbia

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Geoffrey Kondogbia zai koma Inter Milan idan likitoci sun kammala duba lafiyarsa

Kungiyar Inter Milan za ta dauki dan kwallon Faransa, Geoffrey Kondogbia, mai taka leda a kulob din Monaco ta Faransa.

Kondogbia, mai shekaru 22, ya amince da yarjejeniyar kudi da suka kai £25m, yayin da likitocin Inter za su duba lafiyarsa a ranar Litinin.

Dan kwallon wanda aka yi ta rade-radin cewar Manchester City da Arsenal sun yi zawarcinsa, zai buga wa Inter tamaula zuwa shekaru biyar masu zuwa.

Kondogbia ya koma Monaco murza leda ne daga Sevilla ta Spaniya a watan Agustan 2013, a inda ya yi mata wasanni 49.