Juventus ta dauki Mario Mandzukic

Hakkin mallakar hoto juventus.com
Image caption Shekara hudu a jere yana sauya kungiyar kwallon kafa

Kungiyar Juventus ta Italiya ta dauki dan kwallon Atletico Madrid, Mario Mandzukic, kan kudi £13.6m.

Mandzukic, mai shekaru 29, ya koma Atletico taka leda a bara daga kulob din Bayern Munich, yayin da ya ci kwallaye 20 a raga daga wasanni 43 da ya buga wa Atletico tamaula.

Dan kwallon ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru hudu, kuma a kunshin kwantiragin da suka cimma, Juventus za ta iya bashi £15m.

Wannan shi ne karo na hudu da Mandzukic ke komawa kungiyar da aka doke a wasan karshe a kofin Zakarun Turai kai tsaye, bayan da ya koma Bayern a shekarar 2012 da kuma Atletico a bara.

Dan kwallon Juventus mai zura kwallaye a raga Carlos Tevez ana ta rade-radin cewar zai koma Italiya da murza leda.