Keshi zai martaba yarjejeniya da NFF

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na uku kenan da Keshi ke horar da Super Eagles

Hukumar kwallon kafar Nigeria NFF ta ce tana da tabbacin cewar Stephen Keshi zai martaba yarjejeniyar shekaru biyu da suka kulla kan horar da Super Eagles.

A makon jiya ne hukumar kwallon kafar Ivory Coast ta fitar da sunayen mutane sama da hamsin da suke zawarcin horar da kasar, ciki har da sunan Stephen Keshi.

NFF ta ce Keshi wanda ya kulla yarjejeniya da ita a watan Afirilu yana farin ciki da aikin da zai yi da Nigeria.

Ivory Coast tana neman kocin da zai jagoranci tawagar kwallon kafar kasar domin maye gurbin Herve Renard.

Keshi wanda ya jagoranci Super Eagles zuwa lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 2013, ya samu rashin jituwa da NFF, inda har ya taba yin murabus daga aikinsa.