Keshi ya gurfana a gaban kwamitin NFF

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karo na uku da Keshi ke jagorantar Super Eagles

Kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafar Nigeria NFF, ya gana da koci Stephen Keshi kan amsa tuhumar da ake yi masa ta yin zawarcin aikin horar da tawagar kwallon kafar Ivory Coast.

Shi kuwa mai tsaron ragar Super Eagles Vincent Enyeama ya ki ya bayyana gaban kwamitin domin amsa tambayoyi bisa jawabin da ya yi kan wasan da Nigeria ta buga a Kaduna.

Kwamitin amintattu na NFF ne zai yanke hukuncin da zai dauka nan da wata rana da ba a sanar ba.

Hukumar kwallon kafar Ivory Coast ce ta wallafa sunayen mutane sama da 50 da ke zawarcin son horar da kasar, ciki har da Keshi wanda ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu da NFF a watan Afirilu.

Shi kuwa Enyeama ya yi jawabi ne da ya shafi rashin tsaro a Kaduna, a lokacin da Nigeria ta kara da Chadi a wasan neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Afirka a shekarar 2017.

NFF ta bukaci mai tsaron ragar Super Eagles wanda ke taka-leda a Lille ta Faransa da ya yi mata karin bayani kan batun da ya yi, amma bai yi hakan ba.

Golan yana fuskantar hukuncin dakatarwa, bisa karya dokar da'ar 'yan wasan da kuma kin bayyana gaban kwamitin ladabtarwa da ya yi ranar Talata.