An ci kwallaye 263 a gasar Premier Nigeria

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Za a ci gaba da wasannin mako na 14 ranar Lahadi

Bayan da aka kammala buga wasannin mako na 13 a gasar Premier Nigeria a makon jiya, an zura kwallaye 263 daga cikin fafatawa 127 da aka yi.

Chisom Chikatara na kungiyar Abia Warriors da kuma Bright Ejike dake murza leda a Heartland kowannen su ya zura kwallaye bakwai a raga a gasar.

Haka kuma an raba katin gargadi guda 445 da kuma jan katin korar dan wasa daga filin tamaula idan ya yi laifi guda 23 a wasannin Premier Nigeria.

Bayelsa United ce tafi rashin da'a a gasar, yayin da ta karbi kati mai ruwan dorawa guda 27, sannan aka bai wa 'yan wasanta jan kati guda hudu, bayan wasannin mako na 13.

Kano Pillars wacce ke rike da kofin bara ce ta fi da'a a gasar, a inda 'yan wasanta suka karbi katin gargadi sau 27.

Ranar Laadi ake shirin shiga wasannin mako na 14 a filaye daban-dadan a fadin kasar.