Everton ta dauki Gerard Deulofeu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gerard Deulofeu ya buga wa Everton wasa aro a gasar 2014-15

Kungiyar Everton ta dauki dan kwallon Barcelona Gerard Deulofeu wanda ya buga mata tamaula aro a kakar wasan bana a kan kwantiragin £4.3m.

Deulofeu bai samu damar buga wasanni ba a babbar kungiyar Barcelona, a inda ta bayar da shi aro ga Sevilla daga nan kuma ya koma Everton.

Dan wasan, mai shekaru 21, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru uku, kuma zai komo Godison Park ranar I ga watan Yuli.

Tuni kocin Everton Roberto Martinez ya ce Deulofeu zai goge da murza leda a kulob din kuma zai zama fitatcen dan wasa a Premier.