Bolt ba zai yi atisayen tantance 'yan wasa ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bolt yana kokarin dawo da tagomashinsa kafin wasan da za a yi a China

Usain Bolt ya fice daga atisayen tantance 'yan wasan da za su wakiltar Jamaica a tseren mita 100 da kasar ta shirya yi.

Bolt mai shekaru 28 ya fice daga wasannin ne a shirin da yake yi na maido da kuzarinsa domin tunkarar gasar tsere ta duniya da China za ta karbi bakunci.

Dan wasan yana da tikitin halartar wasannin da China za ta karbi bakunci a cikin watan Agusta a matsayin mai rike da kambun tseren mita 100 da kuma na 200.

Bolt ya kasa yin abin azo a gani a tseren mita 100 da kuma 200 da ya fafata a farkon shekarar nan.