Ban yi murabus daga Fifa ba - Blatter

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin wasu jami'an Fifa da cin hanci da rashawa

Shugaban hukumar kwallon kafar Duniya, Sepp Blatter, ya ce bai yi murabus daga shugabancin Fifa ba.

Blatter -- mai shekaru 79 -- ya ce zai yi murabus daga aikinsa a ranar 2 ga watan Yuni, bisa zargin cin hanci da rashawa da suka mamaye hukumar.

Wata jaridar Blick ta Switzerland ta ce Blatter ya ce bai yi murabus ba, illa dai makomarsa da aikinsa na tattare ne a hannun babban taron da hukumar za ta yi a watan Disamba.

Hakan ne ya sa ake hangen watakila Blatter zai sake tsayawa takarar kujerar shugabancin Fifa.

Blatter ya ce har yanzu shi ne ke jagorantar Fifa kuma zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da zai mika bukatunsa a babban taron da hukumar za ta yi.

Dangane da bincike da ake yi a Fifa kan cin hanci da rashawa, Blatter ba zai halarci wasan karshe na cin kofin duniya ta mata da ake yi a Canada ba.