Martivez ya koma kungiyar Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jackson Martinez zai maye gurbin Mandzukic wanda ya koma Juventus murza leda

Dan kwallon Colombia, Jackson Martinez, ya tabbatar da cewar zai koma murza leda kungiyar Atletico Madrid ta Spaniya daga kulob din Porto.

Martinez wanda aka dunga danganta shi da zai koma wasa Arsenal a baya, ya ce ya kammala kulla yarjejeniya da Atletico a ranar Juma a.

Dan wasan mai shekaru 28, ya sanar da hakan ne, bayan da Argentina ta fitar da Colombia daga gasar Copa America a bugun fenariti a wasan daf da na kusa da karshe.

Martinez ya koma Porto a shekarar 2012, a inda ya ci kwallaye 67 daga wasanni 90 da ya buga, kuma shi ne wanda yafi cin kwallaye a raga a gasar a shekaru uku a jere.

Dan kwallon zai maye gurbin Mario Mandzukic wanda ya koma murza leda Juventus na Italiya.