Wikki Tourists ta doke IfeanyiUbah da ci 1-0

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Wikki ta hada maki 26 bayan da ta buga wasanni 14

Kungiyar IfeanyiUbah ta yi rashin nasara a hannun Wikki Tourists har gida da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 14 da suka fafata ranar Lahadi.

Wikki ta zura kwallo a raga ta hannun Chukwudi Samuel saura minti 13 a tashi daga wasan, kuma hakan yasa ta hada maki 26 daga wasannin 14 da ta yi.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Giwa FC ta ci El-Kanemi kwallaye 3-1, yayin da Enyimba ta doke Nasarawa United da ci 2-0 a Aba, sai Akwa da Warri Wolves da suka buga kunnen doki.

Fafatawa tsakanin Kano Pillars da Dolphins ta shi suka yi 2-2, yayin da Sharks da Heartland suka tashi wasa 1-1.

Ga sakamon wasannin mako na 14 da aka buga.

  • Giwa FC 3-1 El-Kanemi
  • FC Ifeanyiubah 0-1 Wikki
  • Sharks 1-1 Heartland
  • Enyimba 2-0 Nasarawa Utd
  • Bayelsa Utd 2-0 Kwara Utd
  • Lobi Stars 2-0 Abia Warriors
  • Akwa Utd 1-1 Warri Wolves
  • Rangers 1-0 Sunshine Stars
  • Kano Pillars 2-2 Dolphins