An dakatar da Jara daga buga wasanni uku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An hukunta Jara bisa nuna halin rashin da'a a lokacin wasa

Hukumar kwallon kafar kudancin Amurka ta dakatar da dan wasan Chile, Gonzalo Jara daga buga wasannin Copa America.

Kazalima, hukumar ta ci tarar dan wasan kudi $7,500

An hukunta dan wasan ne bisa wani faifan bidiyo da aka nuna a akwatin talabijin da ke filin wasan inda Jara ya yi nuni da yatsansa ga bayan Cavani, wanda hakan alamu ne na cin zarafi da batanci.

Cavani ya fusata a inda ya zabga wa Jara mari bayan da alkalin wasa bai dauki mataki kan cin zarafin da aka yi masa ba, lamarin da alkalin wasa ya kore shi daga wasan.

A karshen karawar Chile ce ta kai wasan daf da karshe a gasar, bayan da ta yi nasara da ci daya mai ban haushi.

Haka kuma dan kwallon ba zai buga wasan farko na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Chile za ta buga ba.