Taiwo yana son ya dawo murza leda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Taye Taiwo tsohon dan wasan Super Eagles ta Nigeria

Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Nigeria da AC Milan, Taye Taiwo, na fatan dawo wa ganiyarsa a tamaula, bayan watanni 14 rabon da ya murza leda.

Rabon da Taiwo ya yi babban wasa tun a watan Afirilun 2014 a kulob din Buraspor na Turkiya bayan da kwantiraginsa ta kare.

Dan wasan ya ce yana fatan zai samu kungiyar da zai koma taka leda watakila a kasar Italiya ko Faransa ko kuma Netherlands.

Taiwo ya fara buga wa Super Eagles wasa a shekarar 2004, kuma ya wakilci kasar a gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarun 2006 da 2008 da kuma 2010.

Tauraruwar Taiwo ta fara haskakawa ne a Marseille ta Faransa daga nan kuma ya koma AC Milan ta Italiya, ya kuma buga wa QPR wasanni aro daga baya ya koma Busapor ta Turkiya.