Sherwood ya dauki Wilkins mataimaki

Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Tim Sherwood ya karbi aikin horas da Aston Villa a watan Fabrairu

Kocin Aston Villa, Tim Sherwood ya dauki Ray Wilkins a matsayin wanda zai taimaka masa a kan aikin horas da kulob din.

Wilkins mai shekaru 58 dan birnin Landan wanda ya yi fice a lokacin da yake murza leda ya yi kocin Jordan a kakar bara.

Haka kuma ya taba horas da tsohuwar kungiyar da ya taba takawa leda Queens Park Rangers.

Sai dai kuma Wilkins bai taba yin aiki da Tim Sherwood wanda ya maye gurbin Paul Lambert a Villa Park a watan Fabrairu ba.