Dicks ya shiga cikin masu horas da West Ham

Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Tsohon dan wasan West Ham mai cin kwallaye a raga

Tsohon dan kwallon West Ham, Julian Dicks, ya shiga cikin jerin masu horas da kungiyar a karkashin jagorancin kociya, Slaven Bilic.

Dicks -- mai shekaru 46 -- ya horar da kungiyar kwallon kafa ta mata ta West Ham a kakar wasan bara.

Dicks ya ci kwallaye 65 daga wasanni 326 da ya buga wa West Ham tamaula, a lokacin da ya yi wasa tare da Bilic a kungiyar.

Dan kwallon ya fara yi wa Hammers wasa daga shekarar 1988 zuwa 1993 da kuma karo na biyu tsakanin 1994 zuwa 1999.