Saulley Muntari da AC Milan sun raba gari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Muntari ya buga wa Inter Milan ta Italiya tamaula

Dan kwallon Ghana Sulley Muntari ya amince ya bar kulob din AC Milan bayan da suka cimma yarjejeniya.

Muntari mai shekaru 30 ya koma taka leda a Milan dungurungum a shekarar 2012, bayan da ya fara buga wasa aro a kulob din.

Sauran shekara daya kwantiragin Muntari da AC Milan wanda ya saka hannu a shekarar 2014 ya kare.

Tun a watan Mayu AC Milan ta fara nuna alamun ba ta bukatar dan wasan ya ci gaba da zama a kulob din, bayan da ta ki saka shi a wasan da ta yi da Palaermo a gasar Serie A.

Rabon da Muntari ya buga wa tawagar kwallon kafar Ghana wasa tun a lokacin da kasar ta kore shi daga sansanin 'yan wasa a gasar kofin duniya a Brazil bisa rashin da'a.