Ivory Coast ta fitar da 'yan takarar aikin koci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ivory Coast ce ta lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 2015

Hukumar kwallon kafar Ivory Coast ta fitar da sunayen mutane biyar daga cikin masu son aikin horas da tawagar kwallon kafar kasar.

Cikin wadanda aka fitar da sunayensu sun hada da Patrice Neveu da Paulo Duarte da Michel Dussuyer da Henri Kasperczak da dukkanninsu suka horar da tamaula a Afirka.

Cikon na biyar shi ne Frederic Antonetti wanda bai taba aikin koci da wata kungiya ko tawagar kwallon kafa a nahiyar Afirka ba.

Sama da masu horar da tamaula 50 ne suka yi zawarcin horas da kasar Ivory Coast domin maye gurbin Herve Renard wanda ya yi murabus daga aikin.

Wasu daga cikin masu horas wa da suka yi fice da kuma suka nemi aikin horas da Ivory Coast sun hada da Stephen Keshi da Giovanni Trapattoni da Raymond Domenechda kuma Dave Jones.