Bolt ba zai yi tseren Diamond League ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bolt zakaran tseren mita 100 da kuma 200

Zakaran tseren gudu a wasan Olympic, Usain Bolt, ba zai fafata a gasar tseren Diamond League da za a yi a Paris da kuma Lausanne ba, sakamakon raunin da ya ji.

Mahukuntan da suke gudanar da gasar ne suka fitar da wannan sanarwar a birnin Paris ranar Talata.

Bolt ya fitar da wata sanarwa cewar ya ji takaici da ba zai halarci tseren da za a yi a Faransa da Lausanne ba, amma yana sa ran zai dawo yin atisaye da zarar ya ji sauki daga raunin da ya ji.

Za a fara yin gasar tseren a Paris a ranar Asabar, yayin da za a yi gumurzu a Lausanne a ranar Alhamis.