Southampton ta sallami Dani Osvaldo

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dani Osvaldo shi ne dan kwallon da Southampton ta dauka mafi tsada a tarihi

Kungiyar Southampton ta soke yarjejeniyar da ta kulla da dan wasan da ta dauka mafi tsada a tarihi Dani Osvaldo.

Osvaldo mai shekaru 29, ya koma Southampton daga Roma kan kudi £15m a kuma kan yarjejeniyar shekaru hudu.

Ya kuma koma kungiyar a watan Oktoban 2013, yayin da ya ci kwallaye uku daga wasannin gasar Premier 14 da ya buga.

Southampton ta dakatar da Osvaldo daga buga mata wasanni tun lokacin da ya yi fada da abokin wasansa Jose Fonte a watan Janairun 2014.

Kungiyoyin Bologna da Lazio suna son daukar dan wasan wanda ya buga wa tawagar kwallon kafar Italiya wasanni 14.