Blatter ya ce yana da kyakkyawan lamiri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blatter ya ce zai yi murabus daga Fifa ranar 2 ga watan Yuni

Shugaban hukumar kwallon kafa na duniya Fifa, Sepp Blatter ya ce yana da kyakkyawan lamiri, kuma duk wanda ya kira shi da cin hanci kamata ya yi a kai shi kurkuku.

Blatter mai shekaru 79, ya sanar zai yi murabus daga Fifa, bayan wani bincike da ya sa aka damke wasu jami'an hukumar bakwai kan zargin cin hanci da rashawa.

Blatter ya shaida wa mujallar Bunte ta Jamus cewar bai taba aikata ba dai-dai ba, saboda haka aljanna zai shiga idan ya mutu.

"Duk wanda ya kirani da cin hanci saboda ana zargin hukumata da cin hanci da rashawa, zan kada kaina ne kawai, kuma duk wanda ya ce min haka ya kamata a garkame shi a gidan yari" in ji Blatter.

Hukumar ta Fifa ta shiga tsaka-mai-wuya bayan da aka damke wasu jami'anta bakwai da ake zargi da cin hanci da rashawa.