Inter Milan ta dauki Miranda na Brazil

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Miranda ya buga wa Atletico gasar kofin zakarun Turai

Inter Milan ta Italiya ta dauki dan kwallon Brazail mai taka leda a kulob din Atletico Madrid na Spaniya.

Miranda mai shekaru 30, yana daga cikin 'yan wasan da Atletico ta lashe kofin La Liga na Spaniya a shekarar 2013-14.

Dukkansu kungiyoyin biyu ba su fadi kudin da dan wasan ya saka hannu kan yarjejeniyar ba, amma rahotanni daga jaridun Spaniya sun ce zai kai £10.6m.

Miranda ya wakilci Brazil a gasar Copa America da Chile ke karbar bakunci.

Inter Milan ta kare ne a mataki na takwas a kan teburi a gasar Serie A ta Italiya a kakar wasannin bara.