Adriano ya koma AC Milan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Luiz Adriano ya haskaka sosai a Shakhtar Donetsk.

AC Milan ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Brazil, Luiz Adriano daga Shakhtar Donetsk.

Haka kuma Milan din na gab da kamalla yarjejeniyar daukar Carlos Bacca daga Sevilla.

Adriano mai shekaru 28, ya zura kwallaye 129 tun lokacin da ya soma taka leda a Shaktar.

A kakar wasan da ta wuce ya zura kwallaye 9 a gasar zakarun Turai watau kenan Cristiano Ronaldo, Lionel Messi da Neymar ne kawai suka shiga gabansa.

A wani labarin kuma, dan kwallon Faransa Adil Rami mai shekaru 29 zai bar AC Milan din ya koma Sevilla.