Falcao ya koma Chelsea a matsayin aro

Image caption Falcao ya zura kwallaye hudu a wasanni 29 tare da United

Chelsea ta dauko dan kwallon Monaco, Radamel Falcao a matsayin aro na tsawon kakar wasa daya, amma zai iya komawa kungiyar dun-dun-dun.

Dan kwallon Colombia mai shekaru 29, a kakar wasan da ta wuce ya murza leda a matsayin aro a Manchester United inda ya zura kwallaye hudu cikin wasanni 29.

Falcao zai hade da tsofaffin abokan wasansa a Atletico Madrid watau Thibaut Courtois, Filipe Luis da kuma Diego Costa.

Falcao ya ce "Na ji dadin hadewa da Chelsea."

Dan kwallon ya zura kwallaye 72 a shekaru biyu tare da FC Porto daga 2009 zuwa 2011 kafin ya koma Atletico inda a nan ma ya shafe kakar wasa biyu.

A 2013 kuma, Falcao ya koma Monaco a kan fan miliyan 50.