Nani na gab da koma wa Fenerbahce

Hakkin mallakar hoto
Image caption Nani ya lashe kofuna tare da Fenerbahce

Za a gwada lafiyar dan wasan Manchester United Nani a kungiyar Fenerbahce ta Turkiya bayan kungiyoyin biyu sun amince a kan yarjejeniyar Euro miliyan shida.

Dan shekaru 28, ya koma Old Trafford ne a 2007 daga Sporting Lisbon.

A kakar wasan da ta wuce ya murza leda a matsayin aro tare da Lisbon din inda ya zura kwallaye 11.

Nani ya lashe kofunan gasar Premier hudu da na zakarun Turai daya a United.

Sai dai tun bayan da Sir Alex Ferguson ya bar kulob din, tauraruwar Nani ta daina haskakawa a Old Trafford.