United za ta kara da Aston Villa ranar Juma'a

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a nuna wasu wasannin gasar Premier a ranakun Juma'a

Aston Villa za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan farko na gasar Premier bana 2016-17 ranar Juma'a.

Za a buga wasan ne ranar 14 ga watan Agusta, sakamakon dalilai masu karfi, ciki har dana samun damar nuna fafatawar a talabijin ga mabiya gasar.

Tun farko an tsara karawar ce ranar 16 ga watan Agusta, kuma United za ta buga wasan neman gurbin shiga gasar zakarun Turai a makon gaba da ranar.

Fafatawa a gasar Premier a ranakun Juma'a a kakar bana yana daga cikin yarjejeniyar da mahukuntan gasar suka cimma kan nuna wasannin a Talabijin.

BBC ta nuna wasannin gasar Premier a Talabijin a ranakun Juma'a daga tsakanin shekarar 1983 zuwa 1985.

Kimanin wasanni 10 na gasar Premier gidajen talabijin za su nuna, bisa yarjejeniar da aka kulla kan gasar Premier 2016-17 zuwa 2018-19 da aka saka hannu a watan Fabrairu.