Blatter ya gaji da daukar laifin da bai yi ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sepp Blatter na fama da matsi kan zargin cin hanci da rashawa da ya mamaye Fifa

Shugaban hukumar kwallon kafa na duniya Sepp Blatter ya zargi kasashen Faransa da Jamus da yin matsin lamba wajen fifita bada daukar nauyin gasar kwallon kafa ta duniya ga Rasha da kuma Qatar.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta baiwa Rasha da Qatar damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya da za a shirya a shekara ta 2018 da 2022 a shekarar 2010.

Da yake magana da wata jaridar Jamus Welt am Sonntag, Blatter ya yi zargin cewa tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da takwaransa na Jamus Christian Wulff sun yi kokarin cusa ra'ayi a zukatan wakilan kasashen su gabanin zaben.

Mr Blatter wanda ke fuskantar bincike daga hukumar leken asiri ta FBI game da zargin cin hanci yace ya gaji da daukar laifi akan abin da bai da iko a kansa.

Ranar 2 ga watan Yuni ne Blatter ya ce zai yi murabus daga shugabancin Fifa daga tsakanin Disamba zuwa Maris a lokacin babban taron hukumar da za ta gudanar.