Lukas Podolski ya koma Galatasaray

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Podolsi ya lashe kofin duniya da Jamus a shekarar 2014 a Brazil

Lukas Podolsi ya koma taka leda kulob din Galatasaray na Turkjiya daga Arsenal kan yarjejeniyar shekaru uku kan kudi £1.8m.

Podolski mai shekaru 30, ya koma Arsenal murza leda daga FC Koln a shekarar 2012 kan kudi £11m, ya kuma ci wa Gunners kwallaye 31 daga wasanni 82 da ya yi mata.

Dan kwallon baya samun damar buga wasanni, bayan da Arsene Wenger ya kawo Mesut Ozil da Alexis Sanchez da kuma Danny Welbeck zuwa Arsenal.

Tun kafin nan Arsenal tana da 'yan wasa masu zura kwallo a rada da suka hada da Olivier Giroud da Alex Oxlade-Chamberlain da suke buga mata wasanni.

Shugaban Galatasaray Dursun Aydin Ozbek ya ce sun yi babban kamu, domin sun dade suna son daukar Podolski