Kulob din New York City ya dauki Pirlo

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Ya buga wa Italiya wasanni 115 ya kuma ci kwallaye 13

Dan kwallon Juventus, Andrea Pirlo, ya koma buga gasar Major League ta Amurka da kulob din New York City.

Pirlo mai shekaru 36, ya lashe kofunan Serie A shida a AC Milan da kofunan zakarun Turai biyu a Inter Milan da kofin duniya tare da tawagar kwallon kafar Italiya a shekarar 2006.

Juventus ce ta bai wa dan kwallon damar koma wa Amurka murza leda, bayan da ta soke kwantiragin da suka kulla da saura shekara daya ya kare.

Pirlo zai taka leda a kulob din New York City tare da Frank Lampard na Ingila da kuma dan kwallon Spaniya David Villa.

Haka kuma Pirlo da Lampard za su fara buga wa kulob din wasan farko da Toronto FC a filin wasa na Yankee ranar Lahadi.

Kulob din New York bai sanar da daukar Pirlo ba, yayin da Juventus ta rubuta rahotan komawar dan kwallon Amurka da murza leda a shafinta na Intanet.