Sunshine ce ta daya a teburin gasar Nigeria

Hakkin mallakar hoto sunshinestarstwitter
Image caption Sunshine Stars ta ci gaba da jagorantar teburin Premier

Sunshine Stars ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburi a gasar Nigerian Premier, bayan tashi wasa 1-1 da Lobi Stars da suka yi ranar Lahadi.

Tunde Adeniji ne ya farke wa Sunshine kwallon da Lobi ta zura mata a raga, yayin da Enyimba da Giwa FC suka kasa lashe wasannin su.

Da wannan sakamakon Sunshine ta ci gaba da jagorantar teburin Premier Nigeria da maki 30 cikin wasanni 16 da ta yi.

Enyimba wacce ta dauki kofin Premier sau shida, ta barar da damarta ta haye wa kan teburin, bayan da ta buga 2-2 da Abia Warriors a Aba.

Wikki Tourists ta garin Bauchi tana matsayi na uku a kan teburin bayan da ta buga kunnen doki da Dolphins a Fatakwal.

Kano Pillars wacce ke rike da kofin bara tana mataki na bakwai da maki 25, bayan da ta doke El-Kanemi Warriors a jihar Kano.

Jumulla, bayan da aka buga wasannin mako na 16 a gasar, an ci kwallaye 17 daga cikin wasanni tara da aka fafata a ranar Lahadi.