Balotelli bai halarci atisayen Liverpool ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blotelli ya sha fama da kalubale a Liverpool

Mario Balotelli bai halarci atisayen Liverpool na tunkarar gasar wasannin bana ba, sakamakon hutu da aka ba shi kan rashi da aka yi masa.

Balotelli ya koma sansanin kulob din Liverpool ranar Litinin, bayan da ya kammala hutun kammala gasar bara.

Dan kwallon mai shekaru 24, yana daga cikin 'yan wasan Liverpool da za su tafi atisayen shirye-shiryen tunkarar wasannin bana a Australia.

Kwallaye hudu kacal Balotelli tsohon dan wasan Manchester City ya ci wa Liverpool tun lokacin da ya koma Anfield taka leda a watan Agusta kan kudi £16m.