Southampton ta dauki Cuco Martina

Hakkin mallakar hoto southamptontwitter
Image caption Southampton za ta halarci Austria domin yin atisaye

Kungiyar Southampton ta dauki Cuco Martina daga FC Twente na Netherlands kan kwantiragin shekaru biyu.

Martina mai shekaru 25, zai halarci atisayen da kungiyar za ta yi a Austria domin tunkarar wasannin bana.

Dan wasan ya buga tamaula tsawon shekaru biyu karkashin jagorancin dan uwan Ronald Koeman Erwin a kulob din RKC Waalwijk.

Southampton ta sayar da Nathaniel Clyne ga Liverpool, kuma ba za ta dauki Toby Alderweireld wanda ke buga wasa aro da ita ba.

Kocin Southampton ya ce Manchester United ta yi zawarcin Morgan Schneiderlin, yayin da suka ki sallama mata.