Wimbledon: Murray zai kara da Federer

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Murray ya ce wasan da zai yi da Roger Federer sai an tashi

Andy Murray ya kai wasan daf da karshe a gasar kwallon tennis ta Wimbledon, bayan da ya doke Vasek Pospisil na Canada.

Murray ya samu nasara ne da ci 6-4 7-5 6-4, kuma wannan shi ne karo na shida da ya kai wasan daf da karshe a gasar cikin shekaru bakwai.

A ranar Juma'a ce za'a buga wasan daf da karshe tsakanin Andy Murray da kuma Roger Federer.

'Yan wasan biyu sun fafata a tsakaninsu sau 24, kuma tare suka yi atisaye a fili daya da sanyin safiyar Laraba