Hummels zai ci gaba da wasa a Dortmund

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hummels ya ce ya yi murna da manyan kungiyoyin Turai suka yi zawarcinsa

Mats Hummels wanda aka yi ta rade-radin zai koma Manchester United ya ce zai ci gaba da murza leda a Borussia Dortmund shekara daya.

Hummels mai shekaru 26, wanda ya dauki kofin duniya da Jamus a Brazil, yana daga cikin 'yan wasan da kocin United Louis van Gaal ya yi zawarci.

Dan kwallon ya ce an martaba shi da manyan kungiyoyin kwallon kafar Turai ke ribibinsa, ciki har da United.

Sauran shekaru biyu ya rage kwantiragin da ya saka hannu da Borussia Dortmund a baya ya kare.

Hummels ya lashe kofunan Bundesliga biyu da Dortmund, tun lokacin da ya koma kulob din daga Bayern Munich a shekarar 2009.