An haramta wa Blazer shiga harkokin wasa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Blazer ya ce cin hanci ya yi katutu a hukumar kwallon kafar duniya.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta haramta wa tsohon jami'inta Chuck Blazer shiga harkokin wasanni har abada bayan ya amince cewa ya karbi cin hanci.

Mr Blazer ya shaida wa hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI cewa shi da wasu manyan jami'an hukumar ta FIFA sun karbi cin hanci dangane da bai wa Afirka ta Kudu damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya a shekarar 2010.

Ya amince da aikata laifuka guda goma wadanda suka hada da cuwa-cuwa da halasta kudin haram da kin biyan haraji.

A watan jiya Mr Blazer -- wanda ya wakilci FIFA a rassanta da ke yankin arewaci da tsakiyar Amurka -- ya amince ya nuna wa hukumomin tsaro shaidu da ke nuna cewa akwai matukar cin hanci a FIFA domin ya samu damar kaucewa daurin shekaru 70 a gidan yari.