Fenerbahce za ta dauki Van Persie

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Saura shekara daya ya rage wa dan kwallon a United

Kungiyar Fernerbahce ta Turkiya ta sanar da cewar tana tattaunawa da dan kwallon Manchester United Robin van Persie domin ya buga mata tamaula.

Farnabahcen ce ta sanar a shafinta na twitter cewar ta tuntubi Van Persie da Manchester United kan ya koma Turkiya murza leda.

Van Persie mai shekaru 31, ya koma United ne a shekarar 2012 kan kudi £24m daga kulob din Arsenal.

Dan wasan wanda saura kwantiragin shekara daya ta rage masa a United, ya ci mata kwallaye 26 a lokacin da ta dauki kofin Premier a 2012-13.

Ya kuma ci kwallaye 10 daga wasanni 29 da ya buga karkashin jagorancin Louis van Gaal.

A ranar Litinin ne abokin wasan Van Persie a United Nani ya koma Fenerbahce.