Sevilla ta dauki Steven Nzonzi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nzonzi zai fara taka leda a gasar La liga daga Premier

Steven Nzonzi ya koma taka leda Sevilla daga kulob din Stoke City na Ingila kan kwantiragin £7m.

Nzonzi dan kwallon Faransa, mai shekaru 26, ya koma Stoke buga tamaula daga Blackburn a shekarar 2012, ya kuma buga wasanni 120.

Dan kwallon ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru hudu, da kuma cewar sai an biya £21.5m ga duk kungiyar da take son sayen ssi kafin zamansa ya kare a Sevilla.

Sevilla ta kammala La Ligar bara a mataki na biyar a kan teburi, yayin da ta lashe kofin Europa a watan Mayu.