Wimbledon: Williams da Muguruza a wasan karshe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar Asabar za su buga wasan karshe a gasar Wimbledon

Serena Williams ta doke Maria Sharapova a wasan daf da karshe a gasar Tennis ta Wimledon, za kuma ta kara da Garbine Muguruza.

Williams mai shekaru 33, ta lashe wasan ne da ci 6-2 6-4, kuma karo na 17 kenan da ta doke Sharapova a shekaru 11.

Da wannan nasarar da Williams ta samu za ta kara da 'yar wasan Spaniya Garbine Muguruza wacce ta doke Agnieszka Radwanska.

Wannan ne karon farko da 'yar kasar Spain ta kai wasan karshe a gasar, yayin da Williams za ta buga wasan karshe a babbar gasar tennis karo na 25.

Ranar Asabar ce za su fafata a wasan karshe a gasar cin kofin Wimbledon.