Gyan ya kamalla komawa Shanghai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gyan zai shafe shekaru biyu a China

Dan kwallon Ghana, Asamoah Gyan ya koma kungiyar Shanghai ta China wacce tsohon kocin Ingila Sven-Goran Eriksson yake jagoranta.

Dan shekaru 29, ya koma China ne daga Al Ain ta hadadiyyar daular laraba (UAE) a kan yarjejeniyar shekaru biyu.

Ba a bayyana adadin kudin da aka siyo shi ba amma kafafen yada labarai na China sun ce zai dinga karbar dala dubu 250 a duk mako.

"Ina godiya wannan babban rana ce ga iyalai na da sauran 'yan wasa," in ji Gyan

A cikin shekaru hudu da ya shafe a Al Ain, Gyana ya zura kwallaye 95 a wasanni 83.