“Ina da kyakkyawar alaka da Sterling”

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sterling zai karbi makudan kudade a Manchester City

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce babu rashin jituwa tsakaninsa da Raheem Sterling wanda ke shirin koma wa Manchester City da taka leda.

Rodgers ya ce yana da kyakkyawar alaka tsakaninsa da Sterling wanda zai koma Ettihad kan kudi fam miliyan 49.

Sterling ya ki amincewa ya tsawaita zamansa a Anfield, bayan da aka yi masa tayin za a dinga ba shi fam dubu 100 a duk mako.

Kuma a makon jiya aka rinka rade radin cewar Rodgers da Sterling sun samu sabani a tsakaninsu.

A ranar Asabar Liverpool ta saka sunan Sterling cikin ‘yan wasa 30 da za su buga mata atisayen tunkarar gasar wasannin bana.

Daga baya Sterling ya ce ba zai halarci atisayen ba domin ya samu damar tattaunawa da Manchester City kan batun komawa can da murza leda.