City ta kamalla cinikin Sterling

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana saran Sterling zai haskaka a City

Manchester City ta kammala daukar Raheem Sterling daga Liverpool kan kudi da ake cewa zai kai fam miliyan 49.

Hakan ne ya kuma sa Sterling ya zama dan kwallon da aka saya mafi tsada a Biritaniya.

Sterling ne da kansa ya bukaci barin Anfield, kuma sai biyu Liverpool tana kin sallama tayin da City ta dinga yi, kafin ta sallama a karo na uku.

Kocin City, Manuel Pellegrini ya bayyana Sterling a matsayin "daya daga cikin manyan 'yan kwallo a duniya."

Sterling a yanzu shi ne dan Ingila da ya fi kowanne tsada a tarihi.