‘Stoke tana bukatar fitattun ‘yan kwallo’

Image caption Hughes ya ce zai yi kokari su samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai.

Kociyan Stoke City, Mark Hughes, ya ce kungiyar tana bukatar sayo karin kwararrun ‘yan wasa.

Hughes ya ce zai yi kokari su samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasannin bana.

Kociyan ya kara da cewar sai idan sun dauko shahararrun ‘yan wasa ne za su iya cimma burinsu a gasar.

Stoke ta taya dan wasan Inter Milan Xherdan Shaqiri amma an ki sallama mata shi.

Sai dai kungiyar ta dauko masu tsaron raga Joselu da Shay Given da kuma Jakob Haugaard.

Haka kuma ta dauki masu tsaron baya Glen Johnson da Philipp Wollscheid da dan wasan tsakiya Marco van Ginkel.