An nada Oliseh a matsayin kocin Super Eagles

Image caption Ana saran Oliseh zai haskaka a Nigeria

An nada Sunday Oliseh a matsayin sabon kocin tawagar Super Eagles a Nigeria.

Dan shekaru 40, Oliseh ya maye gurbin Stephen Keshi wanda aka kora a farkon watan July.

"Muna da zaratan 'yan kwallo da za su samar mana sakamako mai kyau a kwallon kafa," in ji Oliseh.

Ya kara da cewar "Kowa na son tawagar Super Eagles ta haskaka."

Shugaban hukumar kwallon kasar, NFF Amanju Pinnick ya ce "Oliseh zai maido da martabar kwallon Nigeria."

Sunday Oliseh ya bugawa Nigeria wasanni 63 inda ya taimakawa kasar ta lashe gasar kofin Afrika a 1994 da kuma gasar kwallon Olympics a 1996.