Ba za a soma wasa tare da Sanchez ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sanchez ya haskaka a kakar wasan da ta wuce

Dan kwallon Arsenal, Alexis Sanchez ba za a soma murza leda tare da shi ba a farkon kakar wasa ta bana ba, saboda nasarar da ya yi tare da Chile a gasar Copa America.

Dan shekaru 26, ya zura kwallaye 25 a kakar wasa ta bana, inda ya taimaki Arsenal ta lashe gasar kofin FA.

Kocinsa Arsene Wenger ya ce "Alexis zai dawo hutu a ranar 3 ga watan Agusta, kuma sai ya shafe makonni uku kafin ya koma kan ganiyarsa."

Kenan Sanchez ba zai buga wasan Community Shield ba tare da Chelsea a ranar 2 ga watan Agusta.

Arsenal za ta buda wasanta na kakar wasa ta bana ne tare da West Ham a ranar 9 ga watan Agusta.