Man United za ta sayar da Valdes

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Valdes da De Gea duk 'yan Spain ne

Manchester United za ta sayar da golanta Victor Valdes, bayan da kocin tawagar Louis van Gaal ya yi zargin cewa golan "ya ki yarda ya bugawa" karamar tawagar.

Dan kasar Spain mai shekaru 33, baya cikin tawagar United wacce ta tafi rangadi a Amurka.

"Ba ya bin umurni na. Babu wuri ga irinsa," in ji Van Gaal

Babban golan United David De Gea mai shekaru 24, ana alakanta shi da koma wa Real Madrid.

Valdes wanda ya lashe kofunan gasar La Liga shida tare da Barcelona, ya koma United ne bayan da ya yi doguwar jinya.