Ana gwada lafiyar Delph a Man City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fabian Delph

Ana gwada lafiyar kyaftin din Aston Villa, Fabian Delph a Manchester City kasa da mako guda bayan da ya ce ba zai bar Villa Park ba.

Dan wasan mai shekaru 25, ana saran zai koma City a kan fam miliyan takwas.

A makon da ya wuce ne Delph ya fitar da sanarwa inda ya ce "Ba zan je ko'ina ba. Zan tsaya a wannan kulob din."

Delph ya buga wa Ingila wasanni shida tun daga watan Disambar bara.

A cikin wannan makon, Manchester City ta kamalla cinikin sayen Raheem Sterling daga Liverpool.