Ba za mu sayar da Pogba ba — Juventus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pogba na da farinjini tsakanin kungiyoyi a Turai

Juventus ta hakikance cewa ba za ta sayar da Paul Pogba ba, duk da cewar Barcelona na zawarcinsa.

Joan Laporta ya ce zai dauko Pogba idan har ya lashe zaben shugaban kungiyar Barcelona.

Darekta a Juve, Giuseppe Marotta ya ce "Barca ba za ta iya sayen sabbin 'yan kwallo ba kuma Juve ba za ta sayar da shi ba."

Dan kwallon Faransan din Pogba wanda tsohon dan wasan Manchester United ne, kwataraginsa za ta kare ne a watan Yunin 2019 a Juventus din.

Wasu rahotanni sun nuna cewar Chelsea da Manchester City ma suna zawarcin Pogba.