Stambouli ya koma Paris St-Germain

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stambouli ya ce da wuya ka bar buga gasar Premier amma ya dace Ya amsa kiran PSG

Dan kwallon Tottenham, Benjamin Stambouli, ya koma murza leda a Paris St-Germain kan yarjejeniyar shekaru biyar kan kudi £6m.

Stambouli ya buga wa Tottenham wasanni 12 tun lokacin da ya koma kulob din daga Montpellier a watan Satumba.

Dan wasan mai shekaru 24, yana daga cikin 'yan kwallon da suka daukar wa Montpellier gasar Faransa a 2012.

Stambouli ya buga wa Montpellier wasanni 129, kafin ya koma taka leda a gasar Premier.