Fury na fatan kawar da Klitschko

Image caption Fury ya ce kowa ya kosa da damben Klitschko domin ya dade yana rike da kambu

Tyson Fury ya ce yana son yaga bayan Wladimir Klitschko daga wasan damben boxing saboda ya gunduri mutane.

Fury da Klitschko za su fafata a damben cin kambun ajin masu nauyi na heavyweight a Dusseldorf ranar 24 ga watan Oktoba.

Fury mai shekaru 26 ya yi wasanni 24 ba a doke shi ba, yayin da rabon da Klitschko ya yi rashin nasara a dambe tun shekaru 11 da suka wuce.

Klitschko shi ne yake rike da kambun WBA da IBF da na WBO wanda rabon da a doke shi tun a 2004, bayan da ya sha kashi a hannun Lamon Brewster.

Damben da Klitschko zai yi da Fury shi ne karo na 28 da zai yi kuma wasa na 19 da zai kare kambunsa tun zamowarsa zakaran duniya.